Ban ce Aisha Aliyu Tsamiya ba ta aikata laifi ba, sannan ban ce sana’ar fim sana’a ce mai kyau ba a addinan ce ba, amman magana ta gaskiya wannan baiwar Allah ta na iya kokarinta wajen kare martabar al’adun mu na Hausawa ta fuskar sanya sutura da kuma irin salon da ta ke takawa a cikin harkar fim.
Aisha Tsamiya ko a fannin rawa ba ta wuce makidi, sannan har yanzu ba ta dauko salon rawa wadda ba irin ta mu ta gargajiya ba, wadda ake yi a dandali ko a wajen shekarawa ba. Haka ma akwai wasu dake ganin ko rawar ma ba ta son yi a cikin fim, kamawa ne kawai take yi.
Akwai mutane da yawa wadanda na ji suna yabon ta da kuma yi mata addu’ar fatan alkairi akan irin yadda take gudanar da sana’arta. Saboda ba ta cika fitowa a fim din da zai zubar da mutuncin ta ko sabawa al’adar ta ba.
Sannan dudda irin daukaka da ta samu al’umma sun shaidi jaruma Tsamiya yarinya ce wadda ba ta da girman kai ko wulakanta dan Adam. Sannan al’umma sun shaidi jaruma Aisha yarinya ce mai yawa fara’a a duk inda ka gan ta.
Don haka nake ganin ina ma a ce sauran jarumai na Hausa fim za su daure su dauki salo irin na jaruma Tsamiya. Domin daukar salo irin nata zai rage gurbacewar al’adunmu ta fuskar sutura da kuma tarbiyyar ya’yanmu masu kallon fim.
Daga karshe Aisha ina rokon Allah ya baki miji nagari ki yi aure ki huta.