Aisha Buhari Ta Goyi Bayan Zanga-zangar Rashin Tsaro A Arewa

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, a ranar Asabar, 17 ga Oktoba, ta daura wani gajeren sako amma mai dauke da ma’anoni da yawa a shafinta na Tuwita @aishambuhari.

Sakon da ta daura na cewa #Achechijamaa watau “A ceci jama’a” Duk da cewa bata bayyana karara wanda take nufi da sakon ba, ta daura sakon tare da hoton mijinta, shugaba Muhammadu Buhari yana zaune da hafsoshin tsaro.

Hakazalika ta hada maganan da waka mai bukatar dauki na ceton Arewa.Wannan shine sakon na farko tun ranar Litinin da ya gabata inda ta raba sanarwan Buhari kan gyara da ake shirin yiwa hukumar SARS.

Shugaban hukumar ‘Yan sanda, Mohammed Adamu, ya sanar da rusa hukumar SARS ranar Lahadi, 11 ga Oktoba sakamakon zanga-zangan da ake yi a fadin tarayya.

A wani labarin, hukumar tsaron farin kaya watau DSS ta tsare masu shirya zanga-zangar yunkurin kawo karshen “rashin tsaro da mulkin kwarai a Arewa.

A jawabin da kakakin gamayyar kungiyoyin arewa CNG, AbdulAzeez Suleiman, ya saki ranar Asabar kuma ya ce an tsare wasu mambobinsu da aka gayyata ofishin hukumar ta DSS domin yi musu tambayoyi amma aka tsaresu daga baya.

Ya ce wadanda aka tsare sune Nastura Sharif, Balarabe Rufai, Aminu adam da Muhammad Nawaila.

Labarai Makamanta

Leave a Reply