Aikin Allah: Gwamnan Zamfara Ya Ba Izala Gudummuwar Naira Miliyan 100

A ranar Litinin ne gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bawa kungiyar ‘Jama’atu Izalatil Bidah Wa Ikamatul Sunna (JIBWIS)’ tallafin N100m domin gina jami’ar Musulunci a jihar Jigawa.

Zailani Bappa, kakakin Gwamna Matawalle, ya bayyana cewa gwamnan ya sanar da bayar da tallafin kudin ne yayin da ya karbi bakuncin shugabancin kungiyar JIBWIS a karkashin shugabanta na kasa, Sheikh Bala Lau, a fadar gwamnatin jihar dake Gusau.

Matawalle ya bayyana cewa babu adadin wani kudi da za a ce ya yi yawa matukar an bayar da shine domin inganta harkar ilimi, musamman ilimin addinin Musulunci. Gwamnan ya yi kira ga abokansa gwamnoni da sauran ma su arziki da su bayar da tallafi ga kungiyoyi ma su kima daraja kamar JIBWIS domin a samu cigaban mutane da kasa baki daya.

“Mun tsinci kanmu a cikin rabuwar kai da kiyayyar juna. Mun zama abokan fada da juna saboda kawai biyan bukatunmu na son rai,” a cewar Matawalle yayin da ya ke gabatar da jawabi.

A cewar gwamnan, bullar kungiyoyin ‘yan bindiga da ke garkuwa da mutane tare da aikata sauran miyagun laifuka alamace da ke nuna cewa akwai karancin kaunar juna a tsakanin mutanen arewa. Matawalle ya kara da cewa mutanen arewa basa kaunar junansu, hakan ya jawo ana amfani da wasu baragurbi daga cikin jama’a domin cutar da ‘yan uwansu.

“Na yi iyakar kokarina wajen ganin na samar da zaman lafiya a cikin jihata. Zan cigaba da kokarin ganin na kare mutanena daga dukkan wani sharri. “Aikinku a matsayinku na Malamai shine bayar da ilimi ga jama’a domin ilimi shine ginshikin gina kowacce al’umma.

Tun da farko, shugaban kungiyar JIBWIS, Sheikh Bala Lau ya shaidawa gwamna Matawalle cewa shi da tawagarsa sun ziyarci jihar Zamfara ne domin ganin wata makaranta da ke garin Shinkafi wacce tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya ba kungiyar JIBWIS kyauta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply