Aiki Muka Za?eka Ka Yi Ba Surutun Allah Wadai Ba – Sheikh Nuru Ga Buhari

Fitaccen Malamin addinin nan na garin Abuja, Sheikh Muhammad Nuru Khalid ya yi martani game da tabarbarewar tsaro a Gwamnatin Buhari.

Anga wani bidiyo inda fitaccen Malamin yake cewa “Zamu shiga Internet mu fadawa duniya, ba zamu iya yin shiru a yanayin da ake ciki ba ana ta kashe mu kamar kiyashi ba wanda zai yi magana.”

“Anan wajen na taba fada nace wallahi kajin gonarsu baka isa kayi masu irin wannan kisan ba, ba gonar [babban] dan Nigeria da zaka je ka kashe kaji 200 haka kawai in ba a kawo naka zabaniyawan Nigeria sun yi maganin ka ba.”

“Amma ana ta kashe mu ba wanda zai yi magana?… Maganin ku ne ma ku ma ai… [talakawa] kune ranar zabe duk ku haukace, ai wallahi jihadi ne…, kiristoci zasu kwace Nigeria…, to shikenan basu kwace Nigeria ba an barta hannun wanda zai zauna ana kashe ku, iya abunda za ayi idan an kashe ku wai sai ace shugaban kasa yayi Allah wadai… wane irin Allah wadai? An zabe shi don yayi Allah wadai ne? An zabe shi don ya dauki mataki ne! Idan ba zai iya daukar mataki ba “comot”

Related posts

Leave a Comment