Majalisar wakilai ta yi barazanar gayyatar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gurfana a gabanta saboda kin amsa gayyatar ta da tawa wasu ma’aikatansa suka yi.
Kwamitin dake kula da asusun ajiyar kudin gwamnati na majalisar ya ce shugabannin ma’aikatun CBN, NNPC, NPA sun ki amsa gayyatar da ta yi musu.
Ya ce akwai wasu harkar kudi ne da ba’a yi bisa ka’ida ba da kuma wasu ayyukan da na wasu ma’aikatun da wadanan hukumomi zasu amsa tambaya akai.
Shugaban Kwamitin, Wole Oke ya bayyana bacin ransa kan kin amsa gayyatar da wadannan shugabannin ma’aikatu suka yi, inda ya ce a aikewa shugaba a sanar da shi hakan dan ya tursasawa wadannan shugabannin ma’aikatu su gurfana a gaban makalisar.