Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar ?an Kwallon Nijeriya, Ahmed Musa Ya Bada Tallafin Naira Milyan Biyu Domin Gina wani katafaren Masallaci a birnin Kano.
Za a gina masallacin ne a makarantar sakandire ta sojoji dake Barikin Bukavo a jihar Kano.
A kwanakin baya ne dai Ahmed Musa ya shelanta cewa ya dawo buga wasan ?wallon kafa a ?ungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars dake Kano.
Masana dai sun bayyana Ahmed Musa a matsayin ?aya daga cikin attajiran ‘yan wasan ?wallon ?afa a duniya wanda tauraron su ke haskawa.