Rahotannin dake shigo mana daga Yola babban birnin jihar Adamawa na bayyana cewar biyar daga cikin ‘yan takara Shida dake neman tikitin tsayawan takarar ?an majalisar dattawan a mazabar yankin Kudancin jihar a jam’iyyar APC sun ki amincewa da sakamakon zaben fidda gwani wanda ya ba Adamu Samila Numan nasara.
A zantawarsa da wakilinmu a Yola Alhaji Sani Jada ?aya daga cikin ‘yan takarar yace zaben da aka yi ranar Lahadi 29-5-2022 akasarin ‘yan takara dama wakilan zaben basa wurin wanda kuma hakan yasa suka rubuta korafinsu ga jam’iyar tasu ta APC da ta dauki matakin sanya ranan sake za?en.
Sani Jada yace idan jam’iyar ta APC ba ta yi Adalci da gaskiya ba to tana iya rasa kujerar ?an majalisar dattawa a yanki na kudancin jihar Adamawa.
Yankin na kudancin jihar Adamawa dai ya kunshi ?ananan hukumomi Tara da suka hada da Tango, Ganye, Jada, Mayo belwa, Demsa, Numan, Lamurde, Guyuk, dakuma karamar hukumar Shelleng.
Hakan na zuwa ne bayan hatsaniyar da ta tashi a daidai lokacin da ake gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan majalisar dattawa a mazabar kudancin jihar biyo bayan zargin daya daga cikin ‘yan takaran wato Adamu Samila Numan da sayan wakilan zaben a lokàcin da ake gudanar da zaben.
‘Yan takaran biyar din da suka ki amincewa da yadda aka gudanar da zaben dai sun hada da Dr Brigget Ziddon, Sanata Grace Bent, Sanata Ahmed Abubakar, Alhaji Sani Jada, da kuma Bala Sanga.