Adamawa: ‘Yan Bindiga Sun Sace Baturen ‘Yan Sanda

Wasu ‘yan bindiga sun sace dan sanda mai mukamin sufeta, matan wasu fitaccen mafarauci da wasu mutane biyu a garin Koma da ke jihar Adamawa kamar yadda The Nation ta ruwaito.

‘Yan bindigan sun sace mutane shidan ne daga gidajensu da tsakar dare a garin na Koma da ke karamar hukumar Jada ta jihar Adamawa.

Majiyarmu ta gano cewa maharan a safiyar ranar Alhamis sun kashe mutum daya da ake tunanin ya zame barazana gare su.

Rahotanni sun ce yan bindigan masu yawa sun shiga garin na Koma sannan suka fara bi gidajen wadanda suke son sacewa daya bayan daya suna daukan su.

Azzaluman nan sun shigo sun tafi cikin kwanciyar hankali ba tare da wani ta taka musu birki ba,” a cewar wata majiya.

Wadanda aka sace din sune Sufeta Yakubu, Hon Bulus Geoffrey (Kansilar mazabar Koma); Hammanjida Hammanjalo; Hajiya Amina, da kuma matan fitaccen mafarauci Mallam Hassan su biyu.

Bisa ga alamu dai yan bindigan sun fi kai wa yan sanda da mafarauta hari ne.

Labarai Makamanta

Leave a Reply