Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa Elisha Abbo ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar ficewar Abbo a yayin zaman majalisar a yau Laraba.
A wasikar, Sanata Abbo ya yi bayanin cewa ya yanke shawaran sauya sheka daga PDP ne saboda salon mulkin gwamnan jihar Adamawa, Umaru Ahmed Fintiri.
A daidai lokacin da kakar za?e ta 2023 ke ?ara ?aratowa, ana cigaba da samun sauye sauyen she?a a tsakanin ‘yan siyasar Najeriya, bisa ga dalilai na ?ashin kai, domin ko a makon da ya gabata Gwamnan jihar Ebonyi Umahi ya shelanta barin PDP zuwa ga jam’iyya mai mulki ta APC.