Adamawa: Kungiyar Ma’aikata Ta Yi Kiran Fara Biyan Sabon Albashi

An kirayi gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da yayi dukkanin mai yiwa da ya aiwatar da albashi mafi karanci wanda hakan zai taimaka wajen karawa ma aikatan kwarin gwiwa a duk lokacin da suke gudanar da aiyukansu.

Shugana kungiyar ma aikatan kananan hujumomi a Najeriya NULGE shiyar jahar Adamawa HammanJumba Gatugal shi yayi wannnan kira a lokacin da yake jawabi a wurin Babban taron kungiyar na jahar karo na bakwai wanda aka gudanar a yola.

HammanJumba Gatugal wanda ya sabon shugaban kungiyar karo na biyu yace aiwatar da albaahin mafi karancin zai baiwa ma aikatan musammanma na kananan hukumomi damar walwala da kuma gudanar da aiyukansu yadda ya kamata ba tare da wata matsalaba.

HammaJumba ya juma tabbatar da cewa zaiyi dukkanin abinda suka dace domin ganin ma aikatan kananan hukumomi su samu mafita daga cikin matsaloli da suke fuskanta.

Gatugal ya kuma shawarci membobin kungiyar da sukasance masu hada Kansu a koda yaushe wanda acewarsa hakan zaitaimaka wajen cigaban kungiyar ba tare da wata matsalaba.

Harwayau HammaJumba yace ya zuwa yanzu kungiyar karkaahin shugabancinsa ta samu hanyoyin kudaden ahiga daban daban wanda hakan yana taimakawa wajen gudanar da aiyukan kungiyar ba tare da wata matsalaba.

Saboda da haka nema kungiyar ta baiwa wadanda sukayi ritaya sommin tabi wadanda suka hada da manyan ma aikata dubu daya da dari bakwai da biyu a yayinda kananan ma aikata suka kai dubu daya da dari biyar da hamsin wanda kuma jimlanau ya kama dubu biyu da dari shida da hamsin da bakwai.

Shima a jawabinsa gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanda mataimakinsa Crouther ceth ya wakilta yace gwamnati zatayi iya kokarinta domin ganin ma aikatan kananan hukumomi sun samu walwal yadda ya kamata.

Shi kuwa anshi bangaren shugaban kungiyar kwadigo N L C shiyar jahar Adamawa Emmanuel Fashe shikam kirayayi da a baiwa kananan hukumomi yancin gashin kansu yadda ya kamata wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban kananan hukumomi dama ma aikatan kananan hukumomin baki daya

Related posts

Leave a Comment