Akalla mutune goma ne suka mutu yayin da talatin suka jikkata sakamakon hadarin da ya auku tsakanin tireloli biyu da sanyi safiyar ranar Asabar a jihar Adamawa.
Jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) sun tabbatar da aukuwar lamarin. Sunce hadarin ya auku ne sakamakon tukin ganganci da kuma gudun wuce kima.
Sunce an killace wadanda suka mutu tare da mika wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Cottage dake garin Mayobelwa.
Ana cigaba da samun yawaitar faruwar hatsarin Mota a Najeriya wanda ke sanadiyyar rasa rayuka da dama, lamarin da jama’a ke dangantawa akan lalacewar hanyoyin kasar.
A karshen makon nan da muke ciki ne muka kawo muku labarin rasuwar ɗan fitataccen malamin addinin musulunci marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam mai suna Abdulmalik Jafar Adam tare da wasu abokananshi ta sanadiyyar hatsarin Mota.
Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya.
Ameen thumma Ameen