Rahoton dake shigo mana daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar Sanata Aishatu Binani ta bayyana cewa ta janye daga shugabancin kwamitin yakin neman zaben Tinubu a jihar Adamawa cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.
A takardar da ta saka hannu da kanta a kai, ta bayyana cewa ta sauka ne har zuwa lokacin da kotun daukaka kara zata yanke hukunci kan karar da ta mika ta hana ta takarar kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa karkarshin Jam’iyyar APC.
“Sanata Aishatu Binani ta sauka daga shugabancin tawagar yakin neman zaben Tinubu da Shettima har zuwa lokacin da kotun daukaka kara zata yanke hukunci. Ana kira ga kwamitin da su hanzarta nada shugaban rikon kwarya a cikin kankanin lokaci.”
Wata majiya kusa da Binani ta sanar da Daily Trust cewa, ta yanke hukuncin sauka daga mukamin a ranar Alhamis bayan ta fusata da kalaman da wani mamban jam’iyyar yayi a kan wasu manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da tsohon Gwamnan jihar Murtala Nyako.