Adamawa: Ana Amfani Da ‘Yan Daba Wajen Ganin Bayan Mulkina – Fintiri

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya zargi wasu ‘yan adawa da daukar nauyin ‘yan ta’adda da bata-gari wurin kawo cikas a mulkinsa.

Fintiri yayi wannan zargin ne cikin ranakun karshen mako yayin da yake duba wasu ayyukansa a Yola, babban birnin jihar ta Adamawa.

“Bai dace ana daukar nauyin bata-gari ba don lalata kayan gwamnati, kamata yayi su zo su ga yadda muke amfani da dukiyar gwamnati wurin yi wa jama’a ayyuka.”

Gwamnan ya ce, adawa mara ma’ana bata taimakon al’umma, ya nuna yadda yake amfani da dukiya wurin yi wa jiharsa aiki, don haka ya cancanci a yaba masa.

Ayyukan da ake kan yi a jihar, wadanda gwamnan yaje da kansa dubawa sun hada da titin Dougire, titin bayan gidan gwamnati, gidajen likitoci, layin Legas gaba da titin barikin sojoji, layin Falu da sauran wurare da ke cikin Kananan hukumonin Yola ta arewa da ta kudu.

Bayan Fintiri ya sanar da hakan ya nuna niyyarsa ta gyara jiharsa, kuma ya lashi takobin komai rintsi sai ya karasa ayyukansa. A cewarsa,.

“Nayi tunanin ‘yan adawa za su zo su duba yadda muke tattalin dukiyar gwamnati wurin gyaran jiha. Duk da yadda bata-gari suka lalata dukiyoyin gwamnati, suka kuma balle ma’adanai a ranar Lahadi da Litinin, wanda hakan ya kawo cikas daga ayyukan.”

Related posts

Leave a Comment