A wani mataki na wanzar da zaman lafiya a faɗin Najeriya an shiryawa ‘yan jaridu bita na kwanaki uku ƙarƙashin jagorancin cibiyar Dar Al Andalus a birnin Yola na Jihar Adamawa.
‘Yan jaridu waɗanda suka fito daga kafafen yaɗa labarai daban daban na ciki da wajen jihar Adamawa ne dai suka halarci bitar haɗi da wasu kungiyoyin addinai daban daban.
An dai gudanar da mukaloli daban daban musammanma irin rawar da ‘yan jaridu za su iya takawa wajen kawo zaman lafiya a faɗin Najeriya baki daya.
Da yake jawabi a yayin kammala bitar Dr Abubakar Alhassan na sashin tsangayar karatun jarida a Jami’ar Bayero dake Kano, yace ‘yan jaridu su kasance masu gudanar da ayyukansu bilhakki da gaskiya da kuma sanya tsaron Allah madaukakin Sarki a zukatansu a duk lokacin da suke gudanar da ayyukan su.
Shima a jawabinsa Mallam Isa Jafar yace bisa yadda ‘yan jaridu suka fahimci irin bita da aka yi musu yana da yakinin cewa ‘yan jaridu zasu bada muhimmiyar gudunmawa wajen magance dukkanin matsalolin da ake samu a tsakanin Al’umma baki daya.
Anashi ɓangaren Dr Aliyu Dawobe shawartar ‘yan jaridun yayi da su kasance masu bada ingantattun rahotanni musammanma a lokacin zaɓe da kuma kaucewa duk abinda zai kawo tashin hankali a lokaci da ma bayan zaɓe.
Shi kuwa shugaban cibiyar ta Dar Al Andalus Dr Bala Muhammed ya bayyana godiyarsa dangane da yadda aka kammala bitan lafiya ba tare da an samu matsala ba.
Wasu ‘yan jaridu da suka halarci taron bitar sun shadawa Wakilinmu farin cikinsu dangane da wannan bita tare da tabbatar da cewa za suyi aiki da abinda aka koya musu domin ganin an samu cigaban zaman lafiya a fadin kasan nan baki daya.