Domin ganin an bunkasa harkoki noma a fadin Najeriya wanda hakan yasa aka shiryawa malamain gona taron karawa juna sani na kwana daya dangane da sanin kimiyyar kasa a bangaren noma.
Taron wanda cibiyar nazarin kimiyar kasa a Najeriya tare da hadin gwiwar jihohin Adamawa da Taraba ta shirya wanda aka gudanar a jami ar Modibbo Adama dake yola.
Adamu Mu azu wanda shine shugaban hukumar ayyukan gona a jihar Adamawa ya shaidawa muryar yanci cewa shirya wannan taro yana da mutukan muhimmanci domin a cewarsa ta hakane za a samu damar fadakar da manoma yanayin kasa da harkokin noma.
Adamu yace manoma da dama basa sanin matsalar da ake samu dangane da kasa to irin wannan taron zai wayarwa manoma kai wajen maida hankali ta sanin yanayi kasan gonakin su.
Ya kuma shawarci Manoman da su kasance masu neman sani a duk lokacin da suka bukaci yin noma ko kuma sun ga abinda basu fahinta ba a gonakin su inda ya kiraye su da su gaggauta zuwa gun malaman gona su shaida musu halin da gonarsu keciki.
Shima anashi jawabi shugaban tsangayar karantar da kimiyyar kasa a Jami’ar Modibbo Adama dake Yola Dr Abubakar Ibrahim bayyana farin cikinsa yayi dangane da shirya wannan taron tare da kiran mahalarta taron da suyi koyi da abunda aka koya musu da kuma isarwa ga wasu domin ganin an samu nasaran bunkasa harkokin noma yadda ya kamata.
Dr Abubajar yace ?umaman yanayi ma yana daga cikin matsaloli da ake samu a bangaren noma don haka ya kamata a maida hankali wajen magance matsalar baki daya.
Wasu mahalarta taron sun shaidawa muryar yanci cewa suna masu farin ciki dangane da wannan taro da aka shirya musu kuma da yardan Allah zasuyi amfani da abunda aka koya musu domin ganin an samu sau?in matsalar kàn harkokin noma a fadin Najeriya.
Wadanda suka gudanar da lekcoci a wurin taron dai sun hada da Dr Hassan Musa, Dr Abubakar Ibrahim da kuma farfesa A M Sadiq wadanda suka gudanar da lekcoci daban daban a bangaren abunda ya shafi yanayin kimiyar kasa da kuma noma.
Malaman gona da damane dai wadanda suka fito daga jihohin Adamawa da Taraba suka halarci taron.