A yayin da aka fuskanci Babban zaben shekarar ta 2023 an kirayi al’umma Musulmi da su kasance masu yin addu’o’i a koda yaushe domin ganin an kammala zaben lafiya da cigaban kasa baki daya.
Shugabar kungiyar Jama’atu Nasaril Islam bangaren mata dake jihar Adamawa Hajiya Amina Bashir ce tayi wannan kira a wajen adu a ta musamman wanda kungiyar ta shirya a Yola.
Hajiya Amina tace shirya irin wadannan addu’o’i yana da mutukan muhimanci don haka ya kamata iyaye su kasance masu shirya addu’o’i da su da yaransu domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen matsalolin tsaro a fadin kasan nan baki daya.
Shima anashi jawabi mai martaba Lamidon Adamawa Dr Barkindo Aliyu Mustafa wanda hakimin Jimeta Muhammed Chubado ya wakilta kiran sauran kungiyoyin addinin musuluncin yayi da suma suyi koyi da shirya irin wadanan addu’o’i na musamman wanda kungiyar Jama:atu bangaren matan suka shirya, ya kuma yaba musu da wannan mijin kokari da sukayi.
Shi kuwa Malam Malami Garba shawartan al’umma Musulmi yayi da su kasance masu sanya tsoron Allah a zukatansu a dukkanin ayyukasu domin samun tsira ranan gobe kiyama.