Adamawa: An Bukaci Jama’a Su Guji Siyasar Kabilanci – Shugaban ‘Yan Kasuwar Arewa

A yayin da ake gudanar da bikin ranar dimukuradiyya a Najeriya an kira yi ‘yan Najeriya da a daina siyasar kabilanci, ?angaranci dama addini domin cigaban dimokura?iyya harma da cigaban Najeriya baki daya.

Shugaban Kungiyar ‘yan kasuwar Arewacin Najeriya Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ne yayi wannan kira a lokacin zantawarsa da wakilinmu a Yola Fadar gwamnatin jihar Adamawa.

Alhaji Ibrahim yace ya kamata ‘yan Najeriya suyi karatun ta nutsu wajen daina siyasar kabilanci ko bangaranci dama addini wanda acewarsa yin siyasar kabilanci ba zai haifawa dimokura?iyya ?a mai ido ba.

Ibrahim ya kuma bayyana cewa tun da aka koma kan turban dimokura?iyya a shekara ta 1999 zuwa yanzu an samu cigaba masu yawa sai dai wasu matsaloli da baza a rasa ba.

86 ya shawarci ‘yan Najeriya da su rungumi dukkanin abinda zai kawo zaman lafiya dama cigaban dimokura?iyya harma da kawo karshen dukkanin matsalar tsaro a fadin Najeriya baki daya.

Harwa yau ya kirayi shuagabanin addinai da su kasance masu wayarwa al’umma kai dangane da illar siyasar kabilanci ko addini. A binda ya kamata ayi dai shine a zabi wanda zai kawo cigaba da gudanar da ayyukan cigaban kasa baki daya.

Related posts

Leave a Comment