Adamawa: An Buƙaci Jama’a Su Taimaki Jami’an Tsaro

Kwamishinan ‘yan sanda reshen jihar Adamawa CP Olugbenga Adeyanju, ya bukaci al’umma a koda yaushe su dinga tallafawa jami’an tsaro da bayanan da zasu taimakawa jamian kawo karshen matsalolin tsaro musamman na makiyaya da manoma.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne Bayan samar da jami’an da zasu taimakawa ‘yan sanda a cikin Al umma domin kare manoma da makiyya daga rikice – rikicen dake faruwa a tsakaninsu.

Kwamishinan ‘yan sandan jahar Adamawa ya ziyarci karamar hukumar Gombi dake jahar Adamawa domin ganawa da masu ruwa da tsaki da sauran mutanen yankin. Tare da bada shawaran bin dukkanin hanyoyi da suka dace domin wanzar da zaman lafiya a yankin baki daya.
Sanarwan hakan na kunshene a cikin wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje wanda aka rabawa manema labarai a yola.

kwamishinan CP Adayanju ya kuma ja kunnen jami’an ‘yan sandan da su gudanar da aiyukansu yadda ya yakamata kuma duk jami’n in da aka samu da cin zarafin jama’a yayi kuka da kansa.

Daga karshe yayi kira na musamman ga sauran hukumomin tsaro da su hada hannu wurin kawar da aiyukan ta addanci a fadin jahar ta Adamawa baki daya.
Shima a nasa jawabin shugaban karmar hukumar Gombi Hon. Engineer Dimas Shekel tare hakimin Gombi Alh. Usman S Fada, sun godewa kwamishinan yan sandan bisa matakin tsaro da ya dauka a fadi jahar baki daya. Kuma sunyi aljawarin bashi dukkan gudummuwar da ya dace wurin ganin an samu ingantaccen tsaro a yankin

Labarai Makamanta

Leave a Reply