Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya sanar da rasuwar surukarsa kuma matar marigayi Lamidon Adamawa Aliyu Musdafa, Hajiya Khadija Aliyu Musdafa.
Hajiya Khadijah ta rasu ne a ranar Litinin, kuma mataimakin shugaban kasar ya misaltata da mace mai kirki da dattako.
Za a binne ta a ranar Talata a garin Yola, babban birnin jihar Adamawa, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019 ya aika da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa da kuma iyalan gidan Musdafa.
Ya wallafa a shafinsa cewa, “Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un, cike da alhini nake sanar da rasuwar suruka ta kuma matar marigayi Lamido Aliyu Musdafa, Hajiya Khadija Aliyu Musdafa. Hajiya Musdafa ta kasance mace mai kirki, mai dattako.
“A madadin iyalaina, Ina mika sakon ta’aziyya ga Lamidon Adamawa Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa da iyalan gidan Musdafa baki daya.
“Ina mika ta’aziyya ga gwamnati da mutanen Adamawa. Za a yi jana’izarta a ranar Talata a garin Yola, ina addu’ar Allah ya gafarta mata kura kuranta ya sanya ta a Aljanna Firdausi.