Sanata mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya a majalisar Dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ya kamata jam’iyyar APC mai mulki ta mika wa yankin kudu tikitin takararta na Shugaban kasa a 2023 domin samun daidaito.
A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, Shekarau ya ce akwai bukatar aikata hakan domin tabbatar da adalci da daidaito da kuma wanzuwar mulkin dimukuraɗiyya.
Da yake magana kan tsarin mulkin karba-karba, Sanata Shekarau ya ce: “A cikin kundin mulkin APC ba a rubuta batun mulkin karba-karba ba, amma ni na amince akwai tsarin mulki na hankali. “Misali yanzu tsarin shiyya-shiyya da ake gudanarwa ai ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, amma tsari ne mai inganci, yanzu babu abin da za ka yi ba ka shigo da wannan ciki ba.
“To haka ma lamarin shugabanci tsakanin kudu da arewa, idan aka yi watsi da wannan to gaskiya ba a yi wa juna adalci ba, kuma ba mu yi wa tarihin kafuwar Najeriya adalci ba. “Ni ina da ra’ayin cewar wajibi ne don kowa ya ji cewar ana yi da shi.”
Da aka tambaye shi kan ko yana ganin akwai bukatar mayar da mulki yankin kudu bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu, Shekarau ya ce: “Sosai ma. Ni ina ganin ya kamata mu yi haƙuri mu jawo ƴan uwanmu na kudu mu da muke daga arewa.
Ka ga ai da aka yi zaɓe, arewa ita kaɗai ba za ta yi ƙuri’ar samar da shugaban kasa ba, kudu ita kaɗai ma ba za ta yi ba, sai mun hadu kuma zaman tare muke. “Ni abin da na yarda da shi shi ne ba ma wai shiyya-shiyya ba, babu wata jiha a Najeriya yau da ba ta da wadanda za su iya yin shugabanci a kasar nan.”
Da aka tambaye shi kan ko baya ganin yin hakan zai sa PDP mai adawa tayi galaba a kansu idan ta fito da dan takararta daga Arewa, sai ya ce adalci shine gaba, kuma nagartar wanda aka tsayar shine zai kai ga nasara.