Mashahurin Malamin addinin musuluncin nan Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya duba halin da al’umma su ke ciki, ya sanya adala da taimakon jama’a domin ?orewar tsaro a Najeriya.
A Karatun tafsirin Kur’ani Mai Tsarki da yake gabatar wa a babban masallacin juma’a na unguwar Tudun Wada Kaduna Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban kasa da gwamnonin jihohi su fito da kudi da nufin ba talakawa kayan abincin da za su ci a watan Ramadan.
“A bude baitul-mali, a saya wa talakawa tireloli na kayan abinci; shinkafa ta rika yawo, ana ba talakawa.” “Ya ku gwamnonin jihohi, ku bude baitul-mali, a saya wa talakawa abinci a lokacin Ramadan. A fitar da dukiyar talakawa, a saya masu abinci saboda Allah.”
Shararren malamin kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’at wa Iqamatus Sunnah ya ba gwamnatin kasar shawarar yadda za a magance matsalar satar mutane. Sheikh Gombe ya ce: “Masu garkuwa da mutane sun addabe ku, ku na ta kashe miliyoyi a kan tsaro domin ku tsare al’umma, amma har yau babu nasara.”
“Ga hanya mai sauki da za ku yi nasara, ku ji tausayin na-kasa, idan ku ka yi haka, Allah zai ji tausayinku.” Sakataren na Jama’atul Izalatul Bidi’at wa Iqamatus Sunnah wanda aka fi sani da Izala, ya ce idan shugabanni su ka tausaya wa talakawansu, to Allah zai jikansu.