Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Nana Atiku, ?ar tsohon Mataimakin Shugaban ?asa, Atiku Abubakar, ta baiwa wani jarumin masana’antar fina-finai ta kudancin Nijeriya, Nollywood, Zubby Michael kyautar fili a Abuja domin taya shi murnar cikar shekara 37 da haihuwa.
Zubby ya wallafa hotunan sa da Nana a shafinsa na instagram, inda ya baiyana cewa ta bashi kyautar filin.
Ya wallafa cewa “kyautar tunawa da ranar haihuwa mafi girma.”
Jarumin ya godewa Nana, wacce mai harkokin filaye da gidaje ce a Abuja, in da ya ce “Nagode Allah Ya yi albarka.”
Ita ma Nana ?in ta wallafa hotunan ta da jarumin inda ta taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa.
“Ina taya jarumin da ya fi kayatar da ni. Namiji mai zuciyar gwal. Ba zan dena samun farin ciki da ga gare ka ba. Allah Ya ci gaba da bu?a maka kamar yadda ka ke taimakon wasu. Kullum ina mai alfahari da kai. Ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ka. Allah Ya sanyawa rayuwar ka albarka,” in ji Nana.