Abuja: Kotu Ta Ba Da Belin Ameerah Dalilin Tabin Hankali

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da matashiyar nan Ameerah Sufyan, wadda ta yi i?irarin cewa wasu mutane sun sace ta tare da wasu mata masu ciki.

Matashiyar ta gurfana ne a kotun majistare da ke Abuja, babban birnin tarayya da safiyar Laraba bisa rakiyar jami’an tsaro.

Daga cikin tuhume-tuhumen da suka yi mata, ‘yan sanda sun zargi Ameerah da tayar da hankali da yi wa rundunar ?age saboda ta ce mutanen na sanye ne da kakin ‘yan sanda.

Sai dai bayan gabatar da tuhuma a kanta al?alin kotun ya bayar da belinta saboda bincike ya nuna tana da lalurar ?wa?walwa.

A ranar 14 ga watan Yuni ne Ameerah ta wallafa sa?o a shafinta na Twitter cewa wasu mutane sanye da kakin ‘yan sanda sun yi awon-gaba da su daga gidajensu a Abuja.

“Mu 17 ne, ciki har da masu ciki uku da yara biyu, amma ba su ga wayata ba,” kamar yadda ta wallafa a shafin nata.

Lauyar da take kare Ameerah ta fa?a wa kotu cewa gwajin da aka yi wa wadda take karewa ya nuna cewa matashiyar na da lalura a ?wa?walwarta.

Bisa wannan dalili ne kuma suka nemi kotun ta ba da belinta, abin da mai shari’ar ya amince da shi.

Sai dai al?alin ya shar?anta wa Ameerah cewa wajibi ne ta dinga kai kanta ga rundunar ‘yan sanda duk wata na tsawon shekara ?aya don tabbatar da tana shan maganin da likitoci suka rubuta mata.

Da take wallafa sa?on na Twitter da misalin ?arfe 1:40 na ranar 14 ga watan Yuni, Ameerah ta ce mutanen sun sace su ne daga ?angarori daban-daban na birnin Abuja.

Ta ?ara da cewa ta tura tasawirar wuraren da ‘yan bindigar ke wucewa da su ga abokan hul?arta ta dandalin WhatsApp don mutane su dinga ganin inda aka kai su.

Da take siffanta mutanen, ta ce: “Yarabawa ne hu?u da Fulani biyu. Sun rarraba mu. Mu bakwai ne a nan. Sun ce ?aya motar za ta tafi Illorin, mu kuma tamu za ta nufi Ibadan ko Ikeja, kamar yadda suka fa?a.”

Wannan sanarwa da matashiyar ta wallafa ta jawo koke-koke da tir da Allah-wadai daga ma’abota Twitter a tsawon wannan rana, inda aka dinga sukar gwamnati da jami’an tsaron Najeriya kafin daga baya Ameerah ta ?aryata kanta.

Kwana uku da wallafa sa?on nata, rundunar ‘yan sanda ta ce ta gano inda take, sannan kuma da alama i?irarin nata ba gaskiya ba ne.

Rundunar ta ?ara da cewa tana binciken matashiyar “kuma za mu sanar da mutane sakamakon bincike da zarar hali ya yi”.

Sai dai kuma, a ranar 20 ga Yunin Ameerah ta ?aryata kanta, tana mai cewa “babu wanda ya sace ta”.

“Da gangan na fita daga gida, na kai kaina wa?annan wurare, na shiga daji kuma na galabaitar da kaina tsawon kwana hu?u haka kawai. Ina neman afuwa, ku yi mani addu’a saboda ina bu?atarta,” a cewar sabon sa?on da ta wallafa.

“Ina neman afuwar jama’a, da ‘yan sanda, abokaina, da dangina saboda ?aryar da na yi musu. Babu wani abu mai kama da haka da ya faru, kawai tunanina ne maras kyawu.”

Related posts

Leave a Comment