Abuja: Ba A Yarda Sallar Idi Ta Wuce Awa Guda Ba – Ministan Abuja

An ba Musulmi mazauna birnin Abuja ƙarfe 8:00 zuwa 10:00 na safe a matsayin lokacin da za su gudanar da Sallar Idi, a cewar wata sanarwa da hukumar FCTA ƙarƙashin ministan birnin ta fitar.

Sannan kuma kada sallar ta wuce tsawon sa’a ɗaya.

Wannan umarni ɗaya ne daga cikin sharuɗan da hukumar Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja (FCTA) ta bayar na gudanar da sallar a yunƙurinta na daƙile yaɗuwar cutar korona.

Kazalika ba za a gudanar da sallar a filin idin Abuja ba na National Eid Prayer Ground da ke kan Titin Umaru Musa Yar Adua.

“An umarci mutane da su gudanar da sallolin a masallatan Juma’ar unguwanninsu,” a cewar sanarwar.

“Dukkanin bukukuwan Idi za a yi su a cikin gidaje sakamakon dokokin da aka saka na rufe wuraren shaƙatawa da wasanni da nisshaɗi suna nan daram.”

Kafa sharuɗɗan sun biyo bayan wani taro ne da Minista Muhammad Bello ya yi tare da majalisar malaman Abuja ta Abuja League of Imams Initiative ranar Litinin.

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya ta ce ranar Juma’a za a gudanar da Idin na Babbar Sallah sannan kuma Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis da Juma’ar a matsayin hutu a ƙasar baki ɗaya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply