Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Abuja: An Damƙe Matashin Da Ya Kwashi Daloli A Majalisa

Wani matashi mai suna Muhammad Kabiru a ranar Juma’a ya fasa cikin majalisar dokokin tarayya inda ya shiga ofishin wani dan majalisar wakilai ya kwashe daloli da wasu kayayyaki.

Wannan abu ya faru da misalin karfe 2:30 na rana inda matashin yayi amfani da wani mukulli na daban.

An zargi Kabiru da kwashe daloli da kayayykin ofis irinsu na’urar kwamfuta, na’urar fotocofi da printer.

An ruwaito cewa Kabiru ya kasance hadimi ga wani dan majalisa daga Jihar Adamawa kuma sannanen mutum ne a majalisar.

Jami’an tsaron majalisar sun gane fuskarsa a bidiyon na’urar CCTV da ta daukeshi yana satar.

An samu labarin cewa dan majalisar da matashin ke yiwa aiki yana kokarin ganin an yi rufa-rufa kawai a manta da lamarin. Bidiyon na’urar CCTV ya nuna matashin lokacin da yake satar.

Exit mobile version