Kimanin mutane 30 ne suka rasa rayukansu bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauka a Gwagwalada cikin Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Yawancin mazauna garin sun rasa gidajen su a sanadiyyar ambaliyar ruwan, wanda aka fara da misalin karfe 3 na safiyar Asabar.
Ruwan ya tafi da yawancin gine-gine da gidaje, yayin da motoci suka shiga cikin hanyoyi daban-daban a cikin birnin. An mayar da hanyar babban titin Abuja/Lokoja gurin bi, yayin da manyan motoci tare da mukudan kaya suka dinga makalewa.
Babbar gadar da ke tsakanin rafin Gwagwalada da gurin aje motocin na Wazobia duk sun nutse.
Mazauna garin Gwagwalada sun bayyana cewa, sun dade ba su sami irin wannan babban tashin hankali ba na ambaliyar ruwa a cikin tsawon lokaci.
Ambaliyar ya hada da mutanen gurin ciran kudi na ATM ɗin dake harabar babban bankin Nijeriya CBN na kan babban titi. Wasu manyan motoci sun makale a yayin da ambaliyar ya mamaye yankin. Ruwan ya mamaye gidajen mutane, yayin da suke ta tserewa don su tsera da rayukan su.
Ruwan saman kamar da bakin kwarya ya tafi da kayayyakin gidajen mutane kamar, katifa, tebur da kayan dafa abinci. Mazauna garin na kallon kayansu suna ta iyo cikin ruwa babu abin da zasu yi akai, yayin da wasu kuma suka koma gefe suna ta kuka.
Har yanzu hukumomin tsaro ba su tantance girman barnar da ambaliyar yayi ba. Wata majiya daga Hukumar Kula da lafiyar hanya ta Tarayya (FRSC) ta tabbatar da cewa, ana kan duba lamarin, kuma za a ayi duk abin da ya kamata don guje wa irin faruwar haka.