Abin Da Na Shaidawa Sarki Charles A Ziyarar Da Na Kai – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a lokacin ganawa da Sarki Charles na III, a fadar Buckingham ya shaida masa cewa ba shi da gida kan sa a Burtaniya.

A lokacin ganawa da ‘yan jarida bayan ganawa da sarkin mai shekara 73, ya ce sarkin ya tambaye shi ne ko yana da gidan kansa a Burtaniya.

Buhari ya ce makusudin ziyara ita ce tattaunawa kan alaka tsakanin kasashen biyu ta fuskar kasuwanci da diflomasiyya.

Ya ce an tsara ganawar ta su ce a baya a Kigali tun kafin ya zama sarki, sai dai a wannan lokaci ne ganawar ta tabbata.

Wannan ce ganawa ta farko tsakanin shugaba Buhari da basaraken tun bayan hawan sa kan karagar mulki.

Bayanai na cewa ganawar ta bai wa shugaban na Najeriya damar taya sarkin murnar hawa mulki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply