Abin Da Baku Sani Ba Akan Najeriya – Hamza Al-Mustafa

Manjo Hamza Al-mustapha yace mafi girman kuskuren da Nigeria tayi shine amfani da dokokin Amurka wanda sam bai dace da Nigeria ba

Ya bada misali da cewa; Amurka kasace wanda bakin haure suka zo suka hadu suka kafata, shiyasa yawanci dokokin Kasar Amurka yafi bada muhimmanci akan kiyaye hakkin baki fiye da ‘yan kasa, irin wannan dokar Nigeria ta karbo daga Amurka

(Misali:
Ku duba ku gani, bakauyen bature kazami lebura, mai cin naman alade daga kasar China zai zo Nigeria aikin kwangila, zaku ga yana yawo tare da rakiyar jami’an tsaro da manyan bindigogi suna bashi kariya, amma ga talakawa can a kauyukan Katsina da Borno an kasa karesu), wannan shine misalin dokokin Amurka

Major Hamza Al-mustapha Yace duk duniya babu wata kasa da Amurka ta dauketa a matsayin abokiya kut da kut kamar Kasar Ingila, amma duk da haka dokokin Kasashen da tsarin mulkinsu ba iri daya bane, sunyi dokokin da ya dace da su, shiyasa suka zauna lafiya, don haka muddin Nigeria na son ta zauna lafiya sai tayi dokar da ya dace da ita

Hamza Al-mustapha yaci gaba da cewa; lokacin da suke mulki tare da marigayi Sani Abatcha, akwai tsarukan da suka tsara wanda zai taimaki Nigeria ta tsayu da kafafunta, yace amma bayan da Abatcha ya rasu, a shekarar 1999 sai aka tattara tsarin akayi watsi dasu aka kawo na Amurka, wanda shine sanadiyyar matsaloli da tashin hankali da fitinar da ake fama da shi yau a Nigeria

Hamza Al-mustapha yace Arewa tana da sarakuna suna shugabanci bisa kyakkyawan tsari tun lokacin bature bai waye ba yana yawo tsirara, amma da turawa suka waye sukazo suka mulkemu, sai aka rusa darajar Sarakunan Kasarnan wanda sune maganin dukkan matsaloli na tsaro da muke fama dashi a yau, shiyasa ake ganin ba daidai ba

Hamza Al-mustapha yaci gaba da cewa; akwai wani abu guda daya tilo, yana nan boye a Arewa maso gabashin Nigeria wanda idan akayi amfani dashi wallahi ya isa a gina sabuwar Kasar Nigeria, yace wannan sirri ne, ba zai fada ba a yanzu saboda gwamnatin ba da gaske take ba

Na so Nigeria ta samu shugaban kasa kamar Hamza Al-mustapha, naso ace kowace gwamnati a Kasarnan ta tafi tare da shi, wannan bawan Allah yana fadin gaskiya, yana da kishi, kuma jarumi ne bai da tsoro

Ina rokon Allah Ya arzurta Nigeria da jarumi irin Hamza Al-mustapha Amin

Labarai Makamanta

Leave a Reply