Shugaban Kamfanin BUA, Alhaji Abdul-samad Rabi’u ya bada kyautar zunzurutun ku?i har Naira biliyan guda ga jami’ar Ibadan (UI) domin gyaran jami’ar da inganta harkokin ta yadda ya kamata.
Alhaji Rabi’u ya bada kyautar ne a wata ziyara da yakai ofishin mu?addashin shugaban jami’ar, Prof. Adebola Babatunde Ekanola, ranar Alhamis.
Abdul-Samad Rabiu, wanda daraktan ala?ar gwamnati a kamfanin BUA, Dr. Aliyu Idi Hong, ya wakilta yace an baiwa jami’ar wannan kyautar ku?inne saboda yadda take gudanar da ayyukanta masu kyau.
A jawabin da yayi lokacin amsar tallafin, mu?addashin shugaban jami’ar ya godewa gidauniyar Abdul-Samad Rabiu (ASR) da gaba ?aya tawagar Kamfanin BUA bisa wannan hu??asa da suka yi.
Prof. Ekanola ya ?ara da cewa hukumar makarantar zata yi amfani da wannan tallafin wajen bada horo ga ?alibanta domin su zama wa?anda za’a yi alfahari da a duniya.