Abacha Ya Yaudari ‘Yan Najeriya Da Sunan Dimokuradiyya – Babangida

A wata tattaunawa da Trust TV ta yi da tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ya yi magana kan yadda Abacha ya yi wa ‘yan Najeriya wayau kuma ya dare madafun iko a shekarar 1993.

Abacha, wanda ya kwatanta da abokinsa nagari, ya yi aiki a matsayin shugaban sojojin kasa a mulkin Babangida kuma daga bisani aka nada shi ministan tsaro a 1990.

“Gwamnatin Abacha ta yi wa ‘yan Najeriya wayau ne ta hanyar faɗin Sun san komai game da zaben 12 ga watan Yuni da sauransu. Sun fara magana kuma suka bayar da kwarin guiwa na watsi da gwamnatin rikon kwarya. Idan muka fatattaki gwamnatin rikon kwarya, za mu dawo da ku kuma mu cigaba da damokaradiyya ta yadda za a kafa gwamnatin farar hula’.

“Sun saka wa jama’a wannan tunanin, haka kuma wasu fitattu a kasar nan. Amma yayin da Abacha ya hau mulki, an dinga kida da rawa kan cewa za a yi zabe. Mu mun sani, hakan ba za ta faru ba.

Babangida ya kara da jaddada cewa, duk da kasancewar su makusantan juna, juyin mulkin Abacha bai ba shi mamaki ba. “Na san ba zai zo a matsayin abun mamaki ba duk da ba na aiki, na san abinda ke faruwa.”

Abacha ya yi aiki a matsayin ministan tsaro kuma ya zama mafi girma a sojojin da suka karbe mulki ta hanyar watsar da gwamnatin rikon kwarya wacce Babangida ya shirya kuma Ernest Shonekan ke jagoranta, lamarin da yasa dole Shonekan ya yi murabus.

A wata sanarwa da ta watsu a ranar 17 ga watan Nuwamban 1993, Abacha ya sanar da kasar cewa ya karbe mulki daga Shonekan sakamakon rashin tabbas na siyasar a lokacin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply