A Yi Gaggawar Bincikar Waɗanda Suka Ɓoye Tallafin CORONA – NLC

Tun bayan samun rahotannin balle manyan shagunan da aka ajiye kayan tallafin korona tare da kwashesu a sassan Najeriya, Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi kira da babbar murya ga gwamnati akan ta zaƙulo jami’an da suka ɓoye wadannan kayayyakin domin fuskantar hukunci, sannan ta bukaci a gaggauta rabar da duk wani sauran kayan tallafin korona da suke jibge a manyan shagunan ajiya da ke fadin kasar nan.

Kazalika, NLC ta yi Alla-wadai da barnatar da kayan tallafin korona da wasu batagari ke yi har yanzu a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da NLC ta fitar ranar Litinin mai taken, ‘NLC ta bukaci a gaggauta raba duk wasu kayan tallafin korona da sauran kayan agaji’.

A cikin jawabin mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa, Kwamred Ayuba Wabba, NLC ta ce; ‘raba kayan zai taimakawa gwamnati wajen rage kuncin rayuwa da jama’ar ke ciki a halin yanzu’. “A bayyane yake cewa wasu jami’an gwamnati sun boye kayan tallafin korona da aka bayar domin a karshe su karkatar dasu.

“An bayar da kayan ne domin a gaggauta rabawa mutane lokacin da aka saka dokar kulle bayan bullar annobar korona.
“Babu wanda ya bayyanawa jama’a dalilin kin raba musu kayan tallafin korona. Wasu daga cikin kayayyakin sun fara lalacewa sakamakon dadewar da suka yi a jibge a shagunan ajiya. “A yayin da muke Alla-wadai da barnata kayan tallafin korona da sauran kayan agaji da aka ajiye, muna ma su nuna kyamar halayen jami’an gwamnati da suka jibge wadannan kayayyaki da aka bayar domin rabawa talakawa a lokacin da suke cikin wahala da kunci.

“Mu na kira ga gwamnatin tarayya a kan ta binciki wadannan jami’ai tare da gaggauta rabar da sauran kayan tallafin korona da suka rage domin ragewa jama’a zafin halin wahalar rayuwa da suke ciki,”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply