A Yau Ne Za’a Yi Bikin Bada Sanda Ga Sarkin Zazzau

A yau Litinin ne 09 ga watan Nuwamba na wannan shekara da muke ciki ta 2020, za’a gudanar da bikin bada sandar mulki ga mai martaba Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli a birnin na Zazzau.

Ahmad Bamalli wanda ya fito daga gidan Sarautar Mallawa ɗaya daga cikin gidajen sarauta huɗu da ake da su a masarautar Zazzau bayan jahadin Shehu Ɗan Fodiyo, zai kasance Sarki na 19 a cikin wannan Daula ta Usmaniyya.

Shirye-shirye sun kankama a filin Alhaji Muhammadu Aminu, wanda aka fi sani da filin Polo a Zariya, domin shirin gudanar da wannan ƙasataicen biki na naɗin mai martaba Bamalli, wanda ɗa ne wurin marigayi Magajin Garin Zazzau Nuhu Bamalli.

Kamar yadda katin gayyatar naɗin Sarautar ya nuna, za a yi taron a filin wasan Polo wanda ake kira da filin Alhaji Muhammadu Aminu da ke karamar hukumar Sabon gari.

Za a fara taron da karfe 10:00 na safiyar ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2020, inda ake sa ran manyan baƙi a cikin da wajen Najeriya za su halarta.

A wata zantawa da BBC Hausa ta yi da Mai martaba sabon Sarki Ahmad Bamalli, ya ce da fari an so a gudanar da bikin bada sandar ne a ranar Asabar 07 ga wata, sai daga bisani aka yanke shawarar mayar da shi ranar Litinin 09 ga wata, domin dacewa da kwanan watan da Sarauta ta bar gidan Mallawa zamanin kakansa Sarkin Zazzau Alu Ɗan Sidi a shekarar 1920 wato shekara 100 daidai kenan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply