A Yankin Bauchi Ta Tsakiya Ya Kamata Gwamna Ya Fito A 2023- Soro

Tsohon kwamishinan kudi na Jihar Bauchi, kuma daya daga cikin matasan yan siyasa dake son Jamiyyar APC ta tsayar da dan takarar gwamna a 2023
daga mazabar Bauchi ta Tsakiya domin adalci a fagen siyasar Jihar.

Tsohon kwamishinan Dokta Manu Soro wanda shine ya ajiye mukaminsa na kwamishinan kudi a cikin wan nan Gwamnati mai ci ta Jamiiyyar PDP a Jihar Bauchi

Manu Soro yayi wannan kirane lokacin taron da akayi a sakatariyar Jamiyyar APC na Jihar Bauchi da masu ruwa da tsaki na Jamiyyar APC daga shiyyar Bauchi ta tsakiya cikinsu harda Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Bauchi Alhaji Abubakar Y suleiman, da kuma Yan majalisun tarayya dana jiha Tsofaffi da masu ci da suka fito daga yankin,

Yace tun lokacin da aka qirqiro Jihar Bauchi a 1976 shiyyoyin kudanci da arewacin Bauchi ne kawai suka riqe muqamin Gwamnan Jihar Bauchi amma daga shiyyar Tsakiya ba wanda ya taba riqe muqamin daga shiyyar Bauchi tatsakiya cikin gwamnoni Shida da akayi Yan asalin jihar, wanda wannan yana nuni da yadda shiyar tasamu koma baya a fagen siyasa, saboda haka yakamata ayi adalci wa shiyyar don asami daidaito.

Soro yace Shiyyar ta tsakiya nada gudummawar da zata bayar don gina Jihar da al’ummar Jihar Bauchi, zasuyi alfahari da ita saboda jin dadin zama don samar da cigaba mai dorewa da za’a yi a cikin Jihar, yace lokaci yayi da za’a ace Yan Shiyyar Tsakiya su sami cikakiyar wakilci kan dukkan al’amuran daya shafi gudanar da mulkin Jihar cikin adalci.

Ya kara da cewa yin haka shine kawai abinda zai tabbatar da siyasar da kowa zai ji ana damawa dashi ba a maidashi saniyar ware ba, kuma kowa zaiji ana masa gaskiya da adalci, da kishin qasa.

Manu soro yace Allah ya albarkaci Jihar Bauchi da albarkatu da kuma dimbin arzikn qasa da za’a iya magance rashin aikin yi a Jihar, sai ya roqi Uwar Jamiyyar ta qasa data samar da yanayin da dukkan wadanda ke sha’awar tsayawa takara qarqashin inuwar Jamiyyar zasu sami damar yin tarurruka da zabubbukan Jamiyyar cikin gaskiya da adalci.

Tun da farko Shugaban Jamiyyar APC dake Kula da shiyyar Tsakiya na Jihar Bauchi Injiniya zakari Dogo yace an maida shiyyar Bauchi ta tsakiya saniyar ware kuma ana kan tattaketa a fagen harkokin siyasar Jihar,

Yace, masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar Jihar sun maida gyara da daidaito, ta yadda za’a sami sauyi mai ma’ana da nagarta.

Injiniya Zakari yace Shiyyar Bauchi ta tsakiya shiyyace mai girma dake bada quri’u da yawa lokutan zabubbuka ya kamata asan girmanta da alherinta domin ayi mata adalci a siyasar Jihar. Ba kullun sai anci an rage sannan a tuna da yankin ba, mundaina tura mota ta tafi ta barmu, muma yayan Jihar Bauchi ne na asali.

Related posts

Leave a Comment