A Shirye Muke Mu Gayyaci Sojin Ketare A Gama Da Najeriya – Shugaban ‘Yan Bindiga

Shugaban ‘yan ta’addan Jihar Zamfara dake yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, Kachalla Turji, ya ce a shirye kungiyarsa take tayi kira da neman goyon bayan kasashen waje don yaki da dagula Najeriya.

An ji yi muryar Shugaban ‘yan ta’adda Turji a cikin wani faifan bidiyo da aka yada a kafar Facebook suna tattauna akan korafe-korafen da suke ci gaba na kashe-kashe, da satar mutane da kungiyoyin masu satar shanu a yankin.

Shugaban ‘yan Bindigar ya yi magana ne akan ?arfin da kungiyar tasa ke dashi da buwayarta, da kuma kokarin da gwamnati ke yi na ganin bayan su ta hanyar raina karfin kungiyar tasu.

Shugaban ‘yan Bindigar ya bayyana hakan ne a yayin ganawar da suka yi da sanannen malamin addinin Musulunci Dakta Ahmad Abubakar Gumi, wanda ya kai ziyara gani da ido a cibiyar ‘yan Bindigar da ke dajin Shinkafi ta Jihar Zamfara.

?an ta’adda Turji wanda ke sanye da kayan boye kamanni, ya fadawa malaman da Dr. Gumi ya jagoranta a kan aikin samar da zaman lafiya, cewa gwamnatin Najeriya bata cika alkawuran da ta ?aukar musu ba.

Ziyarar ta Dr. Gumi na daga cikin kokarinsa na samar da zaman lafiya da kuma wayar da kai ga al’ummomin Fulani da kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin Arewa maso Yamma.

Related posts

Leave a Comment