A Kiyaye: Rigakafin CORONA Na Bogi Ya Shigo Najeriya – NAFDAC

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta ce ta samu rahoton shigo da rigakafin Covid-19 na bogi a Nijeriya.

Babbar Daraktar Hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana haka a lokacin da wani taron ‘yanjarida a ranar Juma’a.

NAFDAC ta yi gargadin kan shigo da rigakafin ba bisa ka’ida ba, tana mai cewa bata karba ko amincewa da wani rigakafin Covid-19 daga masu samar da shi ba zuwa cikin kasar ba.

Adeyeye ta kuma yi gargadin cewa rigakafin na bogi zai iya haifar da cutuka masu kama da cutar Covid-19, tana mai cewa ko amintaccen rigakafin sai an sa ido kan sa, don gano matsalolin da ke tattare da shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply