Saudiyya ta yaye rukunin farko na mata sojoji daga makarantar horar da mata zalla aikin sojin, bayan shafe mako 14 ana basu horo.
Manjo Janar Adel Al-Balawi, shugaban cibiyar ilimantarwa da horas da sojoji ya ce wannan dama ce mai muhimmanci da za ta taimaka wajen sake inganta tsaro.
Sannan ya shaida cewa yana fatan matan za su nuna jajircewa wajen zama ‘yan kasa nagari da kare dokoki da tsare-tsaren da aka dorasu a kai.
Babban hafsan sojojin ƙasar Janar Fayyad bin Hamed Al-Ruwaili ne ya dauki nauyin bikin yaye daliban.
A watan Fabarairu Saudiyya ta bada damar daukan mata aikin soji a Ƙasar.