Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Dokta Muhammad Bello Matawallen Maradun ya bayyana cewa su a Jihar Zamfara suna bukatar jami’an tsaron yan sandan SARS saboda irin aikin da suke gudanarwa a Jihar.
Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan ya fito daga taron kungiyar Gwamnonin Arewacin Nijeriya da aka yi a Kaduna.
Matawalle ya ce su matsayinsu a Jihar Zamfara Shi ne suna bukatar jami’an tsaron yan Sandan SARS sakamakon irin kwazon aikinsu, don haka ya kara da cewa suna bukatar a zakulo su a duk inda suke a kawo masu su a Jihar Zamfara suna bukatarsu.
Kimanin makwanni biyu kenan da gwamnatin tarayya ta sanar da soke rundunar ‘yan Sandan SARS biyo bayan wata ?azamar Zanga-Zanga da ta dake wakana a fadin ?asar.
Sai dai a jawabin da shugaban kasa ya gabatar kai tsaye ga ‘yan Najeriya a ranar Alhamis ya bayyana haramta dukkanin wata Zanga-Zanga a ?asar, biyo bayan