Hukuncin Rataye Abduljabbar Abin Farin Ciki Ne A Duniyar Musulunci – Dr. Mansur Sokoto

Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan mazaunin Jihar Sokoto Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, ya bayyana hukuncin kisa da Kotu ta yanke wa Abduljabbar Nasiru Kabara a matsayin abin farin ciki a duniyar Musulmi gaba ɗaya.

Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi fice wajen yin katoɓara a karatuttunkan sa musanman akan abin da ya shafi rayuwar Annabi Muhammad da Sahabbai.

Lamarin da ya haifar da matsala a Jihar Kano har gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Ganduje ta shirya zaman muƙabala tsakanin Abduljabbar da wasu Malaman Kano, wand a karshe aka yi nasara akan Abduljabbar.

Da yake tsokaci akan hukuncin da Kotun ta yanke kan Abduljabbar Farfesa Mansur Sokoto ya bayyana wannan rana a matsayin ranar farin ciki ga dukkanin musulmi.

(ويومئذ يفرح المؤمنون بنصر الله)
“Rana ce da muminai suke murna da taimakon Allah’.
Allah mun gode maka. Ka kara kare martabar manzonka da iyalansa da almajiransa da masoyansa har ranar tashin alkiyama. Ka tozarta, tare da wulakanta duk mai keta alfarmarsu.
Alhamdu lillah”

Labarai Makamanta

Leave a Reply