Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Gombe na bayyana cewa a wata ziyara da Isa Ali Ibrahim Pantami ya kai zuwa mahaifarsa, ta jawo surutu a kafofin sada zumunta na zamani.
Kwanan nan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ziyarci garin Gombe, hotunan da ya wallafa a X sun tabbatar da farin jininsa.
Ganin yadda Gombawa suke farin ciki da ganin tsohon ministan tarayyar, sai aka fara ba shi shawarar tsayawa takara a 2027.
Masu wannan tunani suna ganin Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami zai iya zama gwamna bayan wa’adin Inuwa Yahaya ya cika.