Tsadar Rayuwa: A Akwatunan Zabe Ya Kamata Ku Nuna Fushi Ba A Zanga-Zanga Ba – Kwankwaso Ga Matasa

IMG 20240506 WA0135(1)

Madugun Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci ‘yan Najeriya da su nemi sauyi ta hanyar dimokradiyya maimakon zanga-zanga. Kwankwaso Ya bayyana hakan ne A cikin wata sanarwa da shi da kan sa ya sanya wa hannu a ranar Jumma’a 26 ga Yuli, 2024 Ya shiga cikin rashin jin dadi da kan kiraye-kirayen zanga-zangar da matasan ke Shirin gudanarwa a duk fa’din Kasar. Sanata Kwankwaso ya jaddada cewa za a iya samun sauyi mai inganci kuma mai dorewa Amma t hanyar karfin zabe.

Cigaba Da Karantawa

Jam’iyyun NNPP, APC Da PDP Sun Kaurace Wa Shiga Zanga-Zanga A Kano

IMG 20240229 WA0298

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa jam’iyyar NNPP mai mulki da na adawa da suka haɗa da APC da PDP a unguwar Dakata, Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jihar Kano sun haɗa kai wajen kauracewa zanga-zangar da ake shirin yi kan matsin rayuwa a fadin kasar nan. Jam’iyyun, ta bakin ciyamonin su na ƙaramar hukumar, sun yi kira ga al’umma da su kauracewa shiga zanga-zangar. A wani taron gangami da aka yi a Dakata Gidan Dagaci a jiya Asabar, Sabo Sambo (NNPP) da Umar Usman Usman (APC)…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Sun Sace Mai Martaba Sarkin Gobir A Sakkwato

FB IMG 1722229110981

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da hana mutane bacci da idanu biyu rufe a wasu sassan Najeriya duk da kokarin da mahukunta ke yi na samun saukin matsalar. Wani abu da ke kara tabbatar da haka shi ne yadda ‘yan bindiga a ranar Asabar su ka sace basaraken daular Gobir da ke Sokoto, Sarkin Gobir na Gatawa Isah Muhammad Bawa. Yanzu haka ‘yan uwa da sauran jama’ar gari na ci gaba da nuna alhini a kan wannan lamari da ya faru da Sarkin Gobir wanda ba da jimawa ba…

Cigaba Da Karantawa

Ba Domin Zuwan Tinubu Ba Da Najeriya Ta Wargaje – Ministan Ayyuka

Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa da Najeriya ta wargaje, idan ba don Allah ya kawo shugaba Bola Tinubu karagar mulki a wannan lokaci mai muhimmanci ba. Ya bayyana hakan ne yayin da ya bukaci matasa da su soke zanga-zangar da suke shirin yi da kuma tallafawa Gwamanti wajen bunƙasa ababen more rayuwa. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin Gwamnatin Tarayya mai taken “Operation Free Roads” a Abuja a karshen mako, Umahi ya bayyana kwarin gwiwar cewa shugaban kasar zai kawo sauyi a kasar idan aka kara…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Kaduna Ta Dauki Matakin Hana Gudanar Da Duk Wata Zanga-Zanga A Jihar

IMG 20240310 WA0186

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya fara ɗaukar matakai da nufin hana zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta mai zuwa. Sanata Uba Sani ya gana da shugabannin hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya, da roki matasa gami da wayar da kan mutane kan illar zanga-zanga Ya ce masu shirya wannan zanga zanga suna da wata ɓoyayyar manufa ta tayar da tarzoma da gurgunta kasuwancin ƴan ƙasa. Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne yayin da matasa ke shirin gudanar da zanga-zanga a…

Cigaba Da Karantawa