Kwalara: Gwamnatin Tarayya Ta Shawarci ‘Yan Najeriya Su Kaurace Wa Shan Fura, Kunu Da Zobo

images (92)

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa dngane da yaduwar cutar kwalara, gwamnatin tarayya ta bukaci ƴan Najeriya da su guji shan abin sha na gida irin su kunu, zobo da fura domin gujewa ɓarkewar cutar kwalara. Karamin Ministan Muhalli, Iziaq Salako ne ya bayar da shawarar a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, a ranar Litinin. Salako ya hori ƴan Najeriya da su ɗauki matakan kariya kamar tsaftace muhallinsu a koda yaushe da zubar da shara yadda ya kamata a wuraren da aka kebe.

Cigaba Da Karantawa

Jirgin Shugaban Kasa: Za A Sayo Wa Tinubu Tsohon Jirgin Da Bankin Jamus Ya Kwace Hannun Wani Balarabe Mai Taurin Bashi

IMG 20240226 WA0252

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Jaridar PREMIUM TIMES na da tabbacin cewa shi ma Jirgin Shugaban Ƙasa da ake ta haƙilon sayo wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, tsoho ne, kuma daga wani Bankin Jamus za a sayi jirgin, wanda Bankin Jamus ya ƙwace daga hannun wani attajirin Balarabe mai taurin-bashi. Jirgin dai samfurin Airbus A330 ne da aka ƙwace daga hannun Balaraben, wanda wani babban dillalin fetur ne da ya kasa biyan bankin wani bashin maƙudan kuɗaɗen da ya ke bin sa. Sai dai…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Sun Yi Wasoson Mata Da Kananan Yara A Mahaifar Karamin Ministan Tsaro Bello Matawalle

IMG 20240421 WA0046

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da yin garkuwa da mutane 47 daga kauyen Danbaza a karamar hukumar Maradun mahaifar ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle. Wani mazaunin ƙauyen, Abdul Danbaza, ya bayyana cewa ƴan bindigar sun mamaye garin da misalin ƙarfe 2:30 na dare ranar Laraba. Ya shaidawa jaridar Leadership cewa maharan sun yi awon gaba da mutane 47 galibi mata da ƙananan yara zuwa cikin jeji. Abdul ya ce ƴan bindigar, waɗanda adadinsu ya kai…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Za Ta Fara Jigilar Jan Nama Da Waken Suya Zuwa Saudiyya

images (99)

Ministan Harkokin Noma na Nijeriya Mohammad Abubakar ya ce Saudiyya ta nuna sha’awar fara shigar da ton 200,000 na naman shanu da ton miliyan ɗaya na waken suya cikin ƙasarta duk shekara daga Nijeriya. Minista Mohammed ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja cewa Saudiyya ta nuna sha’awar hakan ne bayan da Ministanta na Harkokin Noma ya ziyarci Nijeriya tare da yin wasu taruka da ‘yan kasuwa a fannonin noma. “Nuna sha’awar tasu kan wannan batu ke da wuya sai muka fitar da wani tsari da za…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Ba Ta Taba Yin Shugaba Mai Gaskiya Da Rikon Amana Kamar Tinubu Ba – Shettima

IMG 20240504 WA0033

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya roki ‘yan Najeriya wurin kimanta gwamnatin Bola Tinubu a kasar. Shettima ya bukaci ‘yan kasar su yiwa Tinubu adalci yayin kimanta gwamnatinsa duba da kokarin da yake yi wurin daidaita kasar. Shettima ya bayyana haka ne a ran Juma’a 28 ga watan Yunin 2024 yayin wani babban taro a Abuja, Tsohon gwamnan Borno ya ce Tinubu na aiki ba dare ba rana domin ganin ya inganta kasa . Ya kuma ba da tabbacin…

Cigaba Da Karantawa