Yaki Da ‘Yan Bindiga: Muna Samun Matsala Daga Abuja – Gwamnan Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya zargi gwamnatin tarayya da janye sojojin da ke aiki a wuraren da ke fama da matsalar tsaro a jihar Yayin da yake amsa tambayoyi a cikin shirin A Faɗa A Cika da BBC Hausa tare da tallafin gidauniyar Mac Athur ke shirya wa, gwamna Lawal ya ce ”muna zaune a wasu lokuta sai a turo daga Abuja a ce a cire waɗannan jami’an tsaro, to ya zan yi”? Gwamnan ya ce rashin ikon da yake da shi kan jami’an tsaro ne ya sa…

Cigaba Da Karantawa

Dalilina Na Ziyartar Tsohon Shugaban Kasa Buhari – Atiku

IMG 20240316 WA0103

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina. Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya kai ziyarar ne tare da rakiyar wasu manyan abokan siyasarsa. A saƙon da Atiku Abubkar ya wallafa a shafinsa na X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya kai wa tsohon shugaban Najeriyar ziyara ne domin yin ”gaisuwar Sallah” Ziyarar ta Atiku Abubakar ta zo ne kwana uku bayan ya ziyarci tsaffin shugabannin Najeriya, Ibrahim Babangida da…

Cigaba Da Karantawa

Dambarwar Sarautar Kano: Gwamnatin Kano Ta Zargi ‘Yan Sanda Da Nuna Bangaranci

IMG 20240524 WA0093

Gwamnatin jihar Kano ta zargi ƴan sanda a jihar da nuna ɓangaranci a dambarwar masarautar da taki ci taki cinyewa a jihar. Mai magana da yawun gwamnan jihar Mal Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan yayin wata hira da tashar Talabijin ta Channels a ranar Juma’a. Dawakin Tofa ya bayyana muhimmancin dawo da martabar sarautar kano da ya zargi tsohuwar Gwamnatin Ganduje da rusawa. A hannu guda kuma gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya zargi gwamnatin da ta gabace shi da ɗaukar nauyin ‘yan daba a Kano.…

Cigaba Da Karantawa

Dalilan Da Ya Sa Za A Yi Gwanjon Jiragen Shugaban Kasa – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa a yayin da ake ta ce-ce-kuce kan batun sayar da jiragen sama uku na fadar shugaban kasa a Najeriya, gwamnatin ta yi karin haske kan dalilin sayar da jiragen. Gwamnatin ta ce za a sayar da jiragen ne ba don wani abu sai don su jiragen suna da matsalolin da ke ana yawan kashe kudi wajen gyarasu. Mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya kan harkokin watsa labarai, Abdul’Azeez Abdul’Azeez, ya shaida wa BBC cewa, a lokacin da gwamnatin shugaba Bola…

Cigaba Da Karantawa

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Tiriliyan 121 – Hukumar Kula Da Basussuka Ta Kasa

IMG 20240429 WA0024(1)

Ofishin Kula da Basussuka na Ƙasa (DMO) ya bayyana cewa ƙididdigar basussukan da ake bin Najeriya zuwa watan Maris ya kai Naira tiriliyan 121.67, watau kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 91.46 kenan. Babban Daraktan Hukumar DMO, Patience Oniha ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a, a cikin wata sanarwar da ta fitar a Abuja. Oniha ta ce wannan tulin bashi ya haɗa da wanda ake bin gwamnatin tarayya da kuma jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja. Ta ce zuwa watan Maris, adadin basussukan cikin gida da ake bin Najeriya…

Cigaba Da Karantawa