Kaduna: An Harbe ‘Yan Shi’a 6 A Yayin Artabu Da Tawagar Gwamna

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar a yammacin ranar jiya Alhamis ne ƴan SHI’A mabiya Zakzaky suka fito kan titi domin kira ga gwamnati aka a sakar wa malaminsu fasfo ɗinsa na fita kasar waje domin neman magani. Ƴan shi’ar dai sun fito suna faɗin Free Zakzaky fasfo a daidai lokacin da tawagar Gwamnan jihar Nasiru El-Rufa’i ta zo wucewa ta wurin a yankin titin Byepass, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, lamarin da ya haifar da artabu tsakanin su da tawagar Gwamnan tsaro suka…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Na Matsayi Na Takwas A Ayyukan Ta’addanci A Duniya

A cewar rahoton bincike da ake yi gameda ayyukan ta’addanci da aka fitar a wannan shekarar, ya nuna cewar ayyukan ta’addanci a karon farko sun ragu sosai a kasar tun bayan shekarar 2011. Daga tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020, Najeriya na mataki na hudu a jerin kasashen da aka fi samun ta’addanci a duniya, duk da cewa lamarin ya fi kamari a shekarar 2016 da 2015 da kasar ke a mataki na 2. Kungiyoyin masu ta da kayar baya irin su Boko Haram da kuma ISWAP sun yi sanadiyar mutuwar…

Cigaba Da Karantawa

Sabuwar Najeriya: Ba Zan Yi Gwamnatin Hadin Kai Ba – Tinubu

Zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa zai kafa gwamnatin hadin kai domin janyo kowanne bangaren siyasar kasar wajen yin aiki tare.  Wata sanarwar da ya raba wa manema labarai mai dauke da sanya hannunsa ta bayyana Tinubu na cewa bukatarsa ta zarce haka, a matsayinsa na wanda zai yiwa jama’a hidima, yayin da ya bayyana cewar shi da abokan tafiyarsa suna can suna ta tattaunawa da gudanar da tarurruka domin ganin gwamnatinsa ta fara da kafar dama da zarar ta fara aiki. …

Cigaba Da Karantawa