Gwamnatin Tarayya Ta Dage Gudanar Da Aikin Kidaya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana gwamnatin tarayya ta ɗage aikin ƙidayar jama’a da ta shirya fara gudanarwa ranar 29 ga watan Maris zuwa watan Mayu mai zuwa. Ministan yaɗa labaran ƙasar Lai Mohammed ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwar ƙasar da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya jagronta a Abuja fadar gwamnatin ƙasar. Lai Mohammed ya ce matakin ɗage aikin ƙidayar ya zama wajibi ne bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta ɗage zaɓukan gwamnoni zuwa ranar 18 ga…

Cigaba Da Karantawa

Wahala Da Tsadar Rayuwa Sun Karu A Tarayyar Najeriya – Hukumar Kididdiga

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar Kididdiga ta ƙasa ta ce an samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a watan Janairun 2023. Hukumar ta ce ta sanar a ranar Laraba cewa hauhawar farashin kayayyakin ya haura zuwa kashi 21.82 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 21.34 cikin dari a watan Disamba. Rahoton ya yi nuni da cewa hauhawar farashin kaya a shekara ya kai kashi 6.22 bisa ɗari idan aka kwatanta da na watan Janairun 2022, wanda ya kai kashi 15.60. Rahoton ya ce…

Cigaba Da Karantawa