Da Gangan Aka Canza Naira Da Karancin Fetur Domin Haifar Da Tarnaki A Zabe – Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Dan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin cewar da gangan aka ƙirƙiri batun sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar da batun ƙarancin man fetur domin hana gudanar da zaɓen ƙasar da ke tafe. Bola Tinubu ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar a jihar Ogun ranar Laraba. “Ba sa son zaɓen ya gudana. Suna buƙatar hana gudanar da shi. Shin…

Cigaba Da Karantawa

Fifita Kudu Kan Arewa: Gidajen Yada Labarai Na Arewa Za Su Kaurace Wa Tarukan APC

Shugabannin Gidajen Talabijin da Rediyo Shiyyar Arewa sun koka dangane da wariyar da jam’iyya mai mulki ta APC da Kwamitin yakin neman zaben shugaban ƙasa na jam’iyyar ke nuna musu, inda suke fifita gidajen Talabijin da Rediyo na Kudancin Najeriya ta hanyar ba su tallace tallace, amma na yankin Arewa ko oho. “Mun gano cewar Gidajen Talabijin da Rediyo na kudancin Najeriya musamman yankin Kudu maso yamma, su ake fifitawa ta hanyar ba su tallace tallace na jam’iyyar APC da kuma yaƙin neman zaben shugabancin ƙasa na Tìnubu, su kuma…

Cigaba Da Karantawa