2023: Zan Sauya Salon Yaki Da Ta’addanci Idan Na Lashe Zabe – Tinubu

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar ?an takarar shugaban ?asa a inuwar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin sauya salon yakar ‘yan fashin daji da suka addabi mutane idan ya zama shugaban ?asa a 2023.

An ruwaito cewa tsohon gwamnan na Legas ?in ya yi wannan furucin ne a wurin taron tattalin arziki da zuba hannun jari karo na Bakwai da ya gudana a garin Kaduna.

?an takarar kujerar shugabancin ?asa karkashin jam’iyya mai mulki ya kara da cewa yana da tabbacin zai iya jagorantar kasar nan. Haka zalika ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zai magance baki ?aya matsalolin da suka yi wa ?asar nan katutu matu?ar suka dangwala masa kuri’u ya zama shugaban ?asa.

“Idan kuka bar ni a kan dandamalin nan zan ci gaba da kamfe ne, zan roki El-Rufai kar ya bar Najeriya a 2023 domin muna bukatar kwarewarsa a dai-dai wannan lokacin.” “Ina da kwarin guiwar fa?a muku cewa zan iya jagorancin ?asar nan a 2023 idan kuka goya mun baya. Ina da kwarewar shawo kan baki ?aya matsalolin nan kuma na dawo da ?asar nan kan turba mai kyau da ci gaba.”

Related posts

Leave a Comment