2023: Za A Kai El Rufa’i Kotu Idan Bai Nemi Shugabancin ?asa Ba

Kungiyar Nasiriyya a jihohi 21 sun bayyana aniyarsu ta janyo gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya tsaya takarar shugaban kasa a babben Zaben 2023 dake tafe, ko kuma su ?auki matakin zuwa Kotu.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Kaduna, shugaban kungiyar Nasiriyya kuma mataimakin shugaban jam’iyyar APC a Arewa maso yamma, Dr. Garkuwa Ibrahim Babuga, ya ce tuni shirye shirye sun yi nisa na shigar da karar El-Rufai kan kalaman sa nacewa bashi da sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Babuga Ya ce basu da matakin da yafi zuwa Kotu saboda sunyi magana da gwamnan akan maganar amma yayi watsi da bukatar ya watsa musu ?asa a ido.

“Munyi magana da iyayensa da wasu yan uwansa amma bamu samu gamsasshiyar amsa ba. Dole kuto za mu je, domin shi ya fi cancanta Najeriya ta El-Rufai ce 2023.

El-Rufai ya cancanci ya zama shugaban kasa duba da irin aikin da yake yi. “Mutane da dama sun bukaci El-Rufai ya tsaya takara. Ban san wani irin kira yake so a masa ba, Kun dai ga irin ci gaban da ya yi a birnin tarayya Abuja da kuma jahar Kaduna. Shi yafi cancanta da fadar Aso Rock a 2023.

“Muna kira ga dattawan Arewa, da suyi watsi da bambancin jam’iyya, mu hada karfi da kuma gangami don El-Rufai ya tsaya takarar shugaban kasa.

Related posts

Leave a Comment