2023: Wasu Manya Na Burin Tarwatsa Najeriya – Tanko Yakasai

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Dattijon Arewa Tanko Yakassai, ya yi zargin cewa wasu manyan shugabannin arewa biyu na kokarin lalata hadin kan kasar gabanin babban zaɓe dake tafe.

Dattijo Yakasai ya soki kiran da sarkin Daura, Alhaji Umar Farooq Umar ya yi na cewa yan arewa su zabi nasu a babban zaben shekarar 2023 dake tafe.

A sanarwar da ya fitar mai dauke da sa hannunsa, Yakasai ya yi gargadin cewa yana da kyau kowa ya yi watsi da wannan yunkurin na mayar da kasar baya. Ya bayyana cewa a baya, yan siyasa na amfani da wasu masu sarautun gargajiya don wanzar da mummunan kamfen din su, amma yanzu ba za a lamunci haka ba.

A yayin da ya ke kira ga sarkin mai daraja ta daya kada ya bari yan siyasa suyi amfani da shi don wanzar da siyasar kabilanci, Yakassai ya yi zargin tsohon ministan noma, Sani Zangon Daura ya yi kira ga yan arewa su zabi nasu.

A cewar Yakasai, abin da Zango da sarkin suka aikata raba kan al’umma ne, kuma tsohon yayi ne da ba zai haifar da alheri ba.

“Na lura da yunkurin da wasu masu hannu a siyasa ke yi na farfado da tsohuwar al’adar da ‘yan siyasa ke amfani da wasu sarakunan gargajiya wurin yin kamfen don muzanta wasu jam’iyyun a idon al’umma.

“Na ga yunkurin da wadannan manyan shugabannin arewa ke yi na lalata hadin kan Najeriya duk da yanzu na tsufa, akwai sauran kuzari tare da ni da zan iya yaki da irin wannan munanan al’adun a siyasan marasa tsafta a yau.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply