2023: Shugabancin Najeriya Ya Fi Karfin Tsofaffi – Obasanjo

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Ekiti na bayyana cewar tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a ranar Litinin ya yi kira ga tsofaffin ‘yan Najeriya da su ba da dama ga matasa masu tasowa wajen gina Najeriya.

A cewarsa, maimakon su tsaya takara, ya kamata tsofaffi su hada kai da matasa tare da samar musu da ilimi da gogewar da ake bukata domin kawo sauyi ga kasar dake cikin tsaka mai wuya.

Obasanjo ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake magana a taron shekara-shekara na gidauniyar Murtala Muhammed Foundation na 2022 mai taken, ‘Beyond Boko Haram: Addressing insurgency, banditry, and kidnapping across Nigeria’.

A yayin taron, babban bako, gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya ce ya tuna namijin kokari da marigayi tsohon shugaban kasa Murtala ya yi lokacin yana makarantar sakandare a shekarun da marigayi Murtala Mohammed ya jagoranci al’amuran kasar nan.

“Muna bukatar samun hadin gwiwa tsakanin tsararraki. Fayemi yace yana makarantar firamare lokacin Murtala-Obasanjo ke can. Don haka, idan tsararrakin Murtala-Obasanjo suna takara da kai a matsayin gwamna to lallai akwai damuwa.

“Ya kamata tsararrakin Murtala-Obasanjo su koma gefe. Ko wanne irin gogewa da ilimin da kuke da shi, muna iya ba ku, kuma muna iya ba masu zuwa a bayanku, ta yadda duk abin da kuke da shi ku ma mika shi ga masu zuwa a baya kada su fara gasa da ku sai dai ma ku sami damar yin abin da zai sa ku gyara Najeriya ta fi kyau fiye da yadda kuka same ta.”

Related posts

Leave a Comment