A? yayin da ya?in neman za?ukan 2023 na ke ?aratowa, rikici yana ci gaba da dabaibaye manyan jam’iyyun siyasar ?asar na APC da PDP.
T?sohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal ya sha alwashin APC ba ta kai labari ba saboda batun ?an takarar shugaban ?asa da mataimakinsa duk Musulmai ne, a ganinsa mummunan shiri ne na raba kan arewacin ?asar.
Y?a ce ba shi da tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ba ne kawai suke adawa da wannan tikiti na Musulmi da Musulmi na APC a kasar ba dukkanin Kiristoci musamman na Arewa na adawa da hakan.
A? nasa ?angaren, Yakubu Dogara ya ce batun tikitin Musulmi da Musulmi abu ne da ba zai haifar wa APC alheri ba, Dogara ya bayyana ra’ayinsa ne a Abuja ranar Larabar yayin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taron da gamayyar Kiristocin Najeriya ta shirya.
A ?angaren Jam’iyyar PDP a ranar Laraba ne Gwamna Nyesom Wike da tawagarsa suka janye daga kwamitin ya?in neman za?e na PDP saboda ?in murabus ?in da shugaban jam’iyyar ya yi.
G?wamnan da tawagarsa sun ce dole ne jam’iyyar ta mi?a shugabancinta ga ?an yankin kudunci tun da ?an arewa ne ya samu takarar shugaban ?asa a PDP ?in.
W?ani mai sharhi kan al’amuran siyasa kuma ?an jarida a birnin Fatakwal na jihar Rivers, Lekan Ige, ya shaida wa sashen BBC Pidgin cewa masu adawa da tikitin Musulmi da Musulmi din nan a ganinsa ba don sun ?i jinin jam’iyyar suke yi ba, suna yi ne don kare muradun mutane masu mabambantan ra’ayoyi.
Y?a ce ya rage wa jam’iyyar APC ta warware matsalolinta kuma yana da tabbacin za ta yi hakan gabanin za?en da ke tafe.
Y?a ce a za?en 1993 Najeriya ba ta damu da bambancin addini ba a lokacin da aka za?i ?an takarar jam’iyyar SDP Moshood Abiola da mataimakinsa Babagana Kingibe, duk da cewa dukkansu Musulmai ne.
“?Jam’iyyar ta koyi wani abu ne daga wancan yanayi kuma tana duba yadda za ta iya ?inke ?arakar da take da ita a yanzu,” in ji Ige.
I?ge ya ce an ?an tayar da jijiyoyin wuya a lokacin da Abiola ya za?i Kingibe a matsayin mataimakinsa amma ?an jam’iyyar ne suka yi aiki tare don samar da ?an takarar.
Y?a ce ita kuwa PDP, ya rage nata ta tsara dabarun warware matsalolin da take fama da su. Ige ya ce wannan duk siyasa ce, kuma jam’iyyar za ta yi ?o?arin warware rikicin idan dai har suna son yin nasara a za?en shugaban ?asa na 2023.
Y?a ce daga yanzu zuwa watan Fabrairu lokaci mai dan tsawo kuma komai na iya faruwa, wanda a ?arshe za su iya fitowa su ce matsalar cikin gida ce kuma an sasanta.
“?Idan ba su warware matsalar ba kuma, za su kawo tarna?i ga damarmakin jam’iyyun wajen cin za?ukan shekarar 2023,”
2- Ambaliyar Ruwa Na Neman Shafe Birnin Legas
Yayin da mazauna Legas da ke ci gaba da fuskantar matsalar ambaliyar ruwa kowacce shekara, musamman a watannin Maris zuwa Nuwamba, a ‘yan shekarun nan yankin na fama da mummunan matsalar ambaliyar ruwa.
Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da hukumomi a Najeriya ke ci gaba da gargadin aukuwar wata ambaliyar nan da dan lokaci kadan.
Haka zalika masana na ganin cewa birnin na Legas ya fara nutsewa a cikin ruwa, sakamakon matsalar dumamar yanayi.
Tuni gwamnatin Jihar ta sanar da jama’a musamman wa?anda ke ma?wabtaka da bakin ruwa da su yi gaggawar kauracewa yankin domin kaucewa afkawa cikin Iftila’in.
A hannu guda kuma birnin Ha?eja na jihar Jigawa shima yana cikin mawuyacin hali sakamakon matsalar Ambaliyar ruwa da ta addabi yankin, inda jama’ar cikin birnin ke cikin damuwa da tashin hankali gami da fargaba na abin da zai je ya dawo.
Hakazalika wannan Iftila’i na ambaliyar ruwa ya yi ta’adi a Jihar Neja inda ruwan ya lashe ma?abartu da tafiya da tarin gawarwaki a cikin makon da ya gabata a yankin Mariga dake Jihar.
Jihohin Najeriya da dama na fuskantar barazanar faruwar Iftila’in ambaliyar ruwa kamar yadda masana suka fa?i na cewar an jima ba a ga irin wannan Iftila’in a fa?in ?asar ba a tsawon shekaru.